Ghana Yankuna
Taswairar Ghana da ke nuna yankunan (Regions) Ghana guda 16
Hoto:Ministry of Foreign Affairs, Ghana
Gabatarwa
Ghana ƙasa ce mai bin tsarin gwamnatin bai-ɗaya, abin da a Turance ake kira unitary government.
Waɗannan yankuna su ne matakin farko idan aka sauko daga sama zuwa ƙasa. Wato daga gwamnatin tarayya sai su, waɗanda kuma suma gudunmomi suke ƙarƙashinsu.
A yanzu haka, Ƙasar Ghana tana da yankuna goma sha shida da aka sake karkasa su zuwa gundumomi 216. Yankuna su ne kamar haka:
- Ahafo mai cibiya a Goaso
- Ashanti mai cibiya a Kumasi
- Bono East mai cibiya a Techiman
- Brong Ahafo mai cibiya a Sunyani
- Central mai cibiya a Cape Coast
- Eastern mai cibiya a Koforidua
- Greater Accra mai cibiya a Accra
- North East mai cibiya a Nalerigu
- Northern mai cibiya a Tamale
- Oti mai cibiya a Dambai
- Savannah mai cibiya a Damongo
- Upper East mai cibiya a Bolgatanga
- Upper West mai cibiya a Wa
- Western mai cibiya a Sekondi-Takoradi
- Western North mai cibiya a Sefwi Wiaso
- Volta mai cibiya a Ho
Manazarta
Ghana High Commission (Babu Rana). Regions in Ghana. Ghana High Commission Canberra, Australia. An Ciro a 2021 daga shafin: https://ghanahighcom.org.au/site/regions-in-ghana
Ministry of Foreign Affairs And Regional Integration Republic of Ghana (Babu Rana). Regions. An Ciro a 2021 daga shafin: https://mfa.gov.gh/index.php/about-ghana/regions/
The Permanent Mission of Ghana to the United Nations (Babu Rana). Map and Regions of Ghana. An Ciro a 2021 daga shafin: https://www.ghanamissionun.org/map-regions-in-ghana/